13 Yuli 2020 - 11:47
Shugaban kasar Mali Ya Rusa Kotun Kundin Tsarin Mulkin Kasar

Shugaban kasar Mali Bubakar Kaita ya bada sanarwan rusa kotun

(ABNA24.com) kundin tsarin mulkin kasar wanda yake cikin bukutan ‘yan adawar kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya bayyana cewa shugaban ya bayyana haka ne a wani jawabin da ya gabatar a tashar talabijin ta gwamnatin kasar a ranar Asabar da ta gabata.

Shugaban ya ce rusa kotun kundin tsarin mulkin kasar zai bawa ma’aikatar shari’ar kasar damar kafa sabuwar kotun kundin tsarin mulki wacce za’a yi wa gyara kan yadda zata gudanar da ayyukanta.

A cikin makon da ya gabata ne yan adawa a kasar Mali suka gudanar da gagarumin zanga-zanga ta neman shugaban kaita ya sauka daga kan kujerar shugabancin kasar, bayan da ya kasa samar da zaman lafiya a arewacin kasar sannan ya kasa magance matsalolin tattalin arziki da kuma na harkokin siyasar kasar.

342/